Shugaba Buhari ya fallasa wanda ya ke ɗaukar nauyin Kanu da Sunday Igboho

451

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, wani dan majalisar tarayyar kasar nan na cikin gungun mutanen da ke daukar nauyin Nnamdi Kanu da Sunday Igboho wadanda ke rajin ballewa daga Najeriya.

Shugaba Buharin ya fadi haka ne a yayin gabatar da jawabinsa kan cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yanci daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya.

Shugaban ya bayyana bikin samun ‘yancin kan a matsayin wanda ke hada kan al’ummar Najeriya masu mabanbantan kabilu da addinai.

A cewarsa daukacin al’ummar Najeriya sun dunkule wuri guda a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, lokacin da yankunan Gabashi da Yammaci da Arewacin kasar nan suka hadu domin bikin murnar samun ‘yancin kai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan