Damar taimakawa talakan Najeriya ta ƙarewa Buhari – Yahaya Kwande

1523

Tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Switzerland kuma wanda ya yi aiki tare da Sardauna, Sir Ahmadu Bello, wato Yahaya Kwande ya bayyana cewa, babu wani sauran lokaci da ya rage wa shugaba Muhammadu Buhari domin taimakon talakan Najeriya.

Ambasada Kwande ya bayyana haka ne a yayin wata hira da musamman da sashen Hausa na RFI albarkacin cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Tsohon jakadan ya bayyana cewa, a halin yanzu, Buhari ba ya tunanin talaka domin kuwa ta kanshi yake.

Yanzu shi ma tunani yake yi kan abin da zai yi bayan ya kammala, ba yana tunanin talakawa ba ne, abin da bai yi ba a shekaru bakwai da suka gabata, me zai iya yi cikin shekara guda, domin lokacin da ya kamata ya taimaki kasar nan an ba shi shekaru takwas kuma ta kare. Inji Kwande
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar Ambasada Kwande tare da wakilinmu na Jos, Tasiu Zakari.

Tsohon Jakadan ya kara da cewa, a halin yanzu ba ya tutiyar cewa shi dan Najeriya ne ganin yadda al’amura suka lalace a kasar, inda zubar da jini ta zama ruwan dare tamkar babu gwamnati a kasar.

Ambasada Yahaya Kwande

Haka kuma ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta sanya talakawa a gaba, yana mai bada misalin yadda farashin abubuwa suka yi tsada kamar magani.

Har ila yau tsohon jakadan ya bayyana irin yadda talakan Najeriya ke yi wa gwamnati biyayya a zamanin mulkin Sardauna saboda gwamnatin wancan lokacin ta damu da shi ba kamar yadda al’amura suka sauya ba a yanzu.

Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan