Shekaru 61 da Samun Ƴancin Kan Nigeria, Cigaba ko Ci baya?

523

Ina taya kasata Nigeriya murnar ranar samun ƴancin kai daga turawan Burtaniya. Duk da ina sane sarai har yanzu Nigeriya tana cikin shekarun kuruciya domin kuwa haryanzu, shekara 61 take, bata ƙarasa shekarun manyan taka ba, ma’ana shekara 70.

Domin in kaji ana maganar dattajo a Nigeriya dan wannan shekarun ne domin an taba samun shugaban matasa dan shekara 62.

Duk da haka bazan rasa dan abinda zan tofa ba ko da ace bashi da yawa. Na kalli ƙasashen da suke sa’anin mu da wanda suke kannan mu da yayanmu da muka sami yancin kai tare, sai san barka.

Sai na tuna wani littafi da na taba karantawa haka yasa naga cewa ya kamata mukalli me ake kira da cigaba (Development), domin gane ainihin ma’anar tambayar da zamu yiwa kanmu.

Zai fi kyau in ɗaura bayanina kan mahangar masanin nan, Dudley Seers domin fahimtar matakin da Nijeriya ke ciki. Dudley, ya ce, kafin a ambaci ƙasa a matsayin wacce ta samu ci gaba, dole ne sai an samar da amsa ga wadannan tambayoyin:

1. Me ke faruwa da Talauci

2. Me ke faruwa da rashin aikinyi

3. Me ke faruwa ga banbanci tsakanin mata da maza?

Idan waɗannan abubuwan nan guda uku suka yi ƙaranci a cikin al’umma, a kan kira wannan al’umma da wacce ta samu ci gaba.

Amma idan aka samu yawaitar waɗannan abubuwa guda uku a cikin al’umma, a kan kira wannan al’umma da wacce ba ta ci gaba ba.

Koda yake a wani zancen, masani Dudley, ya bayyana cewa, ba wai sai dukkan ukun sun yi ƙamari ba ne sannan za a ce al’umma ba ta ci gaba, duk lokacin da aka samu guda daya daga cikin ukun ya ta’azzara, babu makawa wannan al’umma ba ta ci gaba ba.

  • CITAD ta gano wani ƙauye a Kano da ke cikin gagarumar matsalar rayuwa

    CITAD ta gano wani ƙauye a Kano da ke cikin gagarumar matsalar rayuwa

    Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato Centre for Information Technology and Development (CITAD), ta gano wani kauye a yankin ƙaramar Albasu a jihar Kano da al’ummar wannan kauye su ke fuskantar matsaloli daban-daban. Cibiyar ta CITAD ta rawaito cewa mutanen ƙauyen Yarimari – Hungu da ke cikin ƙaramar hukumar Albasu ta jihar Kano […]


Idan muka kalli Nijeriyarmu da kyau, sai dai mu hadiyi yawu, mu yi ajiyar zuciya idan aka zo maganar talauci.Ƙididdigar masana ta tabbatar da cewa kashi 85% na mutanen Nijeriya na rayuwa ne cikin matsanancin talauci.

Waɗannan kashi 85% din su ne mutanen da Dalar Amurka ɗaya ta fi ƙarfinsu a rana.Ba wai kawai matasa waɗanda ba su da aikin yi ba ne wannan matsanancin talauci ya dabaibaye ba, ta yadda Dalar Amurka ɗaya ta fi karfinsu a rana, wannan hatta a tsakankanin magidanta, waɗanda ke da Iyalai.

Mutumin da Dalar Amurka daya ta fi karfinsa a rana, wanne irin talauci kake tsammani yake ciki, ta ya za a yi ya iya ciyar da iyalinsa, ballantana a yi maganar tufafi da karatunsu.

Bambancin da ake nunawa a tsakanin maza da mata wani abu ne wanda ke matukar addabarmu.

Wannan shi ma a fili yake. Mahaifi ya fi ganin muhimmancin ‘ya ‘yansa maza fiye da mata, saboda yana ganin ai ko ba komai, idan mace ta dan tasa, aure za ta yi ta koma ƙarƙashin ikon wani.

Wannan bahagon tunanin ne ya sa ba a muhimmantar da karatun mata, yawancinsu daga Firamare sun kammala ke nan sai kuma aure, wasu kuma kaɗan su kan yi Sakandare, shi ke nan, ‘yan kalilan ke samun damar zuwa Jami’o’i.

Haka kuma a wuraren aiki, an fi muhimmanta yi wa maza ƙarin girma da bayar da mukamai masu muhimmanci fiye da mata. Saboda har yanzu a Nijeriya a na ganin cewa tunani da kwakwalwar mace ba ɗaya ba ne da ta namiji. Wanda wannan sam ba haka ba ne, wasu matan ma sun fi maza tunani da kaifin basira sau dubu.

Batun rashin aikin yi kuwa a Nijeriya sai dai a shafa fatiha. Saboda ba ma kawai wai ana zancen waɗanda ba su da aiki ba ne, a’a ana batun ma’aikatan da ke rasa ayyukansu alhali ga wasu miliyoyi nan a waje, waɗanda ke zaman jiran tsammanin samun aiki.

Lamarin rashin aiki a Nijeriya na da alaƙa da cin hanci, zalunci da danniya. Mutum ɗaya zai sace dukiyar da za a iya ciyar da ƙananan Hukumomi, mutum ɗaya zai sace dukiyar ma’aikata. Waɗannan na daga cikin dalilan da suka sa har yanzu ba mu ci gaba ba, kuma matuƙar aka ci gaba da tafiya a haka, to babu ranar samun ci gaba a Nijeriya.

Daga Shuaibu Lawan shuaibu37@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan