Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai ta Najeriya MSSN ta karrama Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

1827

Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai ta Najeriya wato MSSN reshen makarantar sakandaren Key Academy da ke yankin Gwarimpa a babban birnin tarayya Abuja ta karrama tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da lambar yabo ta musamman.

Taron karramawar da ya gudana a yau Asabar an yi shi ne bayan da ɗaliban makarantar su ka yi bikin saukar Alkur’ani mai girma na shekarar zangon karatu ta 2020 zuwa 2021.

An baiwa Sanata Rabi’u Kwankwaso wanda shi ne babban uban makarantar ta Key Academy, kyautar karramawar sakamakon irin gudummawar da ya ke baiwa harkar ilimi a ciki da wajen jihar Kano.

Sauran waɗanda aka karrama din sun haɗa da Farfesa Rabatu Abdul – Hamid Malama a jami’ar Abuja da kuma Honarabul Mohammad Jamu Yusuf.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan