Sa Kai Ya Fi Bauta: Za a fara gasar zabga ‘Mari’ a Najeriya

388

Masu shirya wata sabuwar gasa da za a fara a karon farko a Najeriya, sun ce za a fara gasar mare-mare cikin watan Oktoba a Najeriya.

Babban Daraktan kamfanin tsara wasannin na TKK Sports, Abdulrahman Orosanya ne ya bayyana haka, ranar Juma’a a Lagos.

Ya ce ba a dai sa ranar da za a fara ba, amma dai cikin watan Oktoba za a fara, kuma a cikin Disamba za a yi wasannin ƙarshe na cin kofuka.

Orosanya ya ce an ƙirƙiro wannan wasan daddala mari a ƙasar Rasha, amma ƙasar Amurika da ƙasashen Turai su ka zamanantar da shi.

“A yanzu ana gudanar da wannan gasa a Rasha, Amurka, Burtaniya, Poland da Afrika ta Kudu.

“Za a tsara gasar mataki-mataki. Akwai matakin ramammu, tsaka-tsakiya, ƙarti, sai kuma na jibga-jibgan ƙarti.

“A ƙa’ida ba za a kantsama wa abokin gasa mari a cikin ido ba, kuma ba za a mari mutum a muƙa-muƙi ko a kan kunne ba. Kumatu kaɗai za a riƙa falla wa mari da tafin hannu.

Ana yin galaba ne idan an gaura wa mutum mari ya kife ƙasa ko ya nuna an fi ƙarfin sa. Inda gwanaye biyu su ka nuna dauriya da jarunta kuwa, to alƙalin wasa ne zai yanke hukunci.

“Za a horas da ‘yan takarar gasar da alƙalai kafin lokacin fara gasar.”

Rahoton Premium Times

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan