Gwamna Nasiru El-rufai zai rushe gidaje Dubu Goma a birnin Zaria

832

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ta turo dubban jami’an tsaro da motocin rushe gini a wata anguwa dake makotaka da kwalejin koyan tukin jirgin sama dake zariya (College of Aviation Technology) don rushe anguwar da ake zargin su da mallakar filayen ba tare da ka’ida mallakar fili ba.

Mazauna yankin unguwar da abin ya shafa sun bayyanawa wakiliyar jaridar Leadership ra’ayinsu akan batun.

Malam Gunji Makama shi ne mai unguwar wani ɓangare a unguwar ya tabbatar da cewa matakin da gwamna Nasiru El-rufai zai dauka a yankin unguwar ta Gres Land ya saɓawa dokar ƙasa.

Mai unguwar ya tabbatar da cewa mafi yawan gidajen da ke wannan yankin suna da takardunsu wanda gwamnati ta ba su.

Gunji Makama ya ƙara cewa ko a lokutan baya hukumar kula da gidaje sun zo domin daukar mataki mai kama da hakan amma sai al’umar unguwar suka garzaya kotu don dai-daita al’amarin.

Ya zuwa yanzu tuni gwamnatin jihar ta turo motocin rushe gini tare da gamayyar jami’an tsaro masu yawan gaske.

Wani sakamako bincike ya tabbatar da cewa a kalla mutane sama da dubu dari 2 ne za su rasa gidajensu in har rusau din ya tabbata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan