Jami’ar Bayero da ke Kano za ta samarwa da ɗalibanta ayyukan yi

393

Jami’ar ta Bayero da ke Kano ta tabbatar da ƙara lokacin dawowa makaranta, daga ranar 4 ga watan Oktoba zuwa makon farko a cikin watan Nuwambar shekarar 2021.

Jawabin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban tsangayar al’amuran ɗalibai Farfesa Shamsudden Umar, ya tabbatar da cewa ƙarin ya shafi har biyan kuɗin makarantar ɗalibai.

Farfesa Shamsuddeen Umar ya ƙara da cewa ɗaliban da ba su biya kuɗin ba su sha kuruminsu, ko da sun ga lokacin da aka saka a shafin jami’ar ya wuce, to akwai tabbacin cewa za a ƙara buɗe shafin.

Haka kuma Farfesan ya yi wa ɗalibai wani sabon albishir na cewa jami’ar za ta fito da wasu sababbin hanyoyi, ta yadda ɗalibai masu sha’awa da kuma dama, za su dinga gudanar da wasu ayyuka a jami’ar, ita kuma jami’ar tana biyansu a duk mako, domin ƙarfafa musu guiwa da kuma samun abin da zai taimaka musu a wajen karatun nasu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan