Jawabin ƴar gidan marigayi Sheikh Ja’afar ya sanya shugabannin Izala zubar da hawaye

1983

Shugaban Kungiyar Izala ta JIBWIS a Najeriya Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa jawabin da Malama Zainab Ja’afar Mahmud Adam ta yi a lokacin da ta ke karɓar shugabancin kungiyar NISA’U SUNNAH reshen jihar Kano ya sanya mahalarta taron zubar da hawaye tare da kabbara.

Shaikh Bala Lau ya bayyana hakan ne a yau Lahadi a shafinsa na Facebook tare da hotunan taron gabatar da sabon shugaban ƙungiyar NISA’U SUNNAH reshen jihar Kano da aka gudanar.

TSARKI YA TABBATA GA ALLAH”


A lokacin da ƴar mu Malama Zainab, wacce ƴa ce ga marigayi Shaikh Ja’afar Mahmud Adam ta ke jawabi ta ke gabatar da jawabin karɓar shugabancin kungiyar NISA’U SUNNAH reshen jihar Kano, ku san gabaki ɗayan mutanen da su ke gurin sun yi kabbara tare da zubar da hawaye. Allah ya yi mata albarka ya yi wa mahaifinta tukwici da gidan aljannar Fiddausi

Ƙungiyar NISA’U SUNNAH wani ɓangare ne na ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS).

Amira Zainab Ja’afar Mahmud Adam

Shaikh Ja’afar Mahmud Adam fitaccen addinin Musulunci ne da ya yi shuhura wajen harkokin koyarwa tare da tafsirin Alqur’ani mai girma.

Wani ɓangare na taron NISA’U SUNNAH

Haka kuma ya rasa rayuwarsa ne a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 bayan da wadansu ƴan bindiga suka harbe shi yayin da yake jagorantar Sallar Asuba a mallasaci da ke birnin Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan