Ma’abota amfani da Facebook, Instagram da WhatsApp sun shiga damuwa sakamakon katsewa da shafukan suka yi a faɗin duniya.A
A yammacin jiya Litinin ne dai shafukan suka tsaya cak a dukkan faɗin duniya, abin da ya haifar da asarar miliyoyin naira ga musamman mamallaka shafukan da kuma sauran jama’a.
Kafofin sun daina aiki a birnin Washington na Amurka da Paris da Landon da sauran biranen duniya, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.
Wannan matsala dai ta shafi masu amfani da shafukan a Najeriya.
Ɗaya daga cikin shugabannin Facebook ya faɗa a Twitter cewa suna ƙoƙarin gano matsalar da daidaitawa cikin gaggawa.
Turawa Abokai