Ganduje Ya Ware Biliyan 3.9 Don Gina Hanyoyi A Masarautun Kano

1078

Gwamnatin jihar Kano ta bada kwangilar gina hanyoyi a masarautun Rano, Gaya da Ƙaraye dake jihar a kan kuɗi naira biliyan 3.9.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba, ya bayyana haka ga manema labarai ranar Lahadi a Kano.

Mista Garba ya ce za a yi aikin gina hanyoyin ne da nufin haɓaka tattalin arziƙin jihar Kano da kuma kawo gwamnati kusa da jama’a.

Ya ƙara da cewa Majalisar Zartwa ta Jihar Kano ta kuma amince da ware ƙarin naira miliyan 42.3 don gina tashar kan tudu a Dala da kuma mahaɗar hanyoyi Zawaciki dake ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan