Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da fara biyan ɗalibai jami’a masu nazarin aikin koyarwa a jami’o’in gwamnati naira N75,000 a duk zangon karatu.
Haka kuma, ɗalibai masu nazarin Shaidar Koyarwa ta Najeriya, NCE, za su riƙa samun naira N50,000 a duk zangon karatu a matsayin wani yunƙurin gwamnati na jawo mutane masu ƙwaƙwalwa a ɓangaren koyarwa.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya sanar da haka a yayin Bikin Ranar Malamai ta Duniya, da aka yi a Eagle Square, Abuja.
Adamu, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa, Sonny Echono ya karanta jawabinsa, ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya za ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi da su tabbatar an samar wa ɗalibai da suka karanta aikin koyarwa aikin yi da zarar sun kammala karatu.
“Ɗalibai masu karatun digirin farko na B.Ed / B.A. Ed/ BSc. Ed a jami’o’in gwamnati za su fara karɓar tallafin naira N75,000 a duk zangon karatu masu NCE kuma za su riƙa samun naira N50,000.00 a duk zangon karatu.
“Gwamnatin Tarayya za ta fito da tsarin da gwamnatocin jihohi za su samar wa ɗaliban NCE aiki da zarar sun kammala karatu”, in ji Mista Adamu.