Dole Ganduje Ya Biya Jaafar Jaafar Tarar N800,000— Kotu

639

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta ce dole Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya biya jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar diyyar naira 800,000 a matsayin tara.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a S.B Namalan ne ya yanke wannan hukunci ranar Litinin.

Alƙalin ya ce Gwamna Ganduje ba zai samu damar sauraro daga kotu ba matuƙar bai biya tarar ba kafin kotu ta ƙara ɗaga ƙarar.

Lauyar Gwamna Ganduje, Lydia Oyewo, ta nemi afuwar kotun kuma ta yi alƙawarin tattaunawa da Gwamnan don bin umarnin kotun.

Gwamna Ganduje ya maka Mista Jaafar da Daily Nigerian a kotu ne sakamakon wallafa wasu faya-fayan bidiyo da suka nuna Gwamnan yana karɓar dalar Amurka a matsayin cin hanci daga ‘yan kwangila.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan