Hukumar EFCC ta bayar da belin Hafsat Abdullahi Umar Ganduje

440

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayar da belin mai dakin Gwamnan jihar Kano Hajiya Hafsatu Ganduje wadda aka fi sani da Gwaggo, bayan da aka tsare ta a ofishin hukumar dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Hukumar EFCC ta kama Hafsatu Ganduje ne bayan da danta yayi korafin tayi sama da fadin wasu kudaden filaye a jihar Kano. Abdulaziz Ganduje shi ne ya rubuta koken ga hukumar EFCC yana mai zargin mahaifiyarsa da wawure kudin mutane na filaye.

Hukumar dai tayi nasarar yin awon gaba da Hafsatu Ganduje a ranar Litinin, inda aka tsare ta na wasu awanni inda daga bisani aka bayar da ita a matsayin beli.

Da sanyin safiyar Talatar nan ne dai aka ga Gwaggo tare da mai gidanta Gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje suna saukowa daga jirgi a filin tashi da sauka na Malam Amini Kano bayan da aka karbo belinta.

Lokacin da Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ke sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan