Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan ta kama Hajiya Hafsat uwargidan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, kan tuhuwar rashawa da zambar fili da ɗanta ya kai kararta.
Wata majiya daga fadar gwamnatin jihar da ta buƙaci a sakaya sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin.
Majiyar ta ce jami’an hukumar EFCC ne suka je har Kano suka kuma tafi da “Goggo” kamar yadda ake kiran ta, zuwa Abuja, don amsa tambayoyi.
Amma ya ce tuni aka kammala kuma har ta koma gida.
Turawa Abokai