Ranar Malamai Ta Duniya: Yadda Ilimi ke fuskantar barazana a arewacin Najeriya

175

Kowacce ranar 5 ga watan Oktoba na matsayin ranar Malamai a sassa daban daban kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware don girmamawa ga malaman da kuma tuna irin gudunmawar da suka bai wa Al’umma baya ga lalubowa tare da magance matsalar da bangaren ilimi ke fuskanta.

Kamar kowacce shekara a wannan karon ma ranar Malaman ta bana ta mayar da hankali kan yadda za a habaka irin gudunmawar da malaman ke bai wa al’umma tare da dakile matsalolin da ke tunkaro harkokin ilimi a matakai daban-daban.

Taken ranar Malaman na bana shi ne ”Malamai a tubalin farfado da ilimi daga nakasu” taken da ke nuna bukatar da ake da shi ta hada hannu wajen farfado da harkokin ilimi musamman a kasashen da ke fuskantar koma baya a fannin karatu.

Wani Malami a bakin aiki

Sai dai bikin na bana yana zuwa a lokacin da masana ke bayyana fargaba kan makomar ilimi a ƙasar nan ganin yadda batun sace-sacen dalibai ke kara ta’azzara musamman a arewacin kasar.

Masanan na ganin matuƙar mahukunta ba su gaggauta shawo kan lamarin ba, zai iya haddasa gagarumar koma-baya wajen ci gaban ilimi a yankin.

Wasu rahotanni sun nuna cewa akwai kimanin dalibai dubu daya da yan bindiga suka sace tun daga watan Disamban bara zuwa wannan lokaci. Ko a cikin watan Disamban bara sai da ƴan bindiga suka sace ƴan makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina su fiye da 340.

Ba a yi nisa ba a cikin watan Fabrairun wannan shekarar ƴan bindigan suka sake sace daliban sakandaren mata ta Jangebe da ke jihar Zamfara su fiye da 300 kuma a cikin watan Yuli suka sace daliban sakandaren Kagara su 27.

A cikin watan Maris na wannan shekarar da aka sace dalibai 37 a makarantar nazarin gandun daji ta Afaka da ke jihar Kaduna.

Wasu ɗaliban makarantar Firamare

Haka ma a cikin watan Afirilu na kunshe da labari marar dadi na sace daliban Jami`ar Greenfield da ke jihar Kaduna.

Sai kuma watan Mayun wannan shekarar, inda nan ma aka sace daliban Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina a jihar Niger su fiye da dari, ciki har da kananan yara `yan shekara uku da haihuwa.

Kazalika, a watan Yunin da ya wuce ma an sa ce daliban kwalejin gwamnatin tarayya da ke Yauri a jihar Kebbi, inda har zuwa yanzu mahukunta ba su fadi aihinin adadinsu ba.

Sai kuma a baya-bayan nan, satar daliban sakandaren Bethel Baptist da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna wadanda su ma mahukunta ba su fadi yawansu ba, amma wasu shaidu sun ce akalla sun kai 130.

Mahukunta a Najeriya dai na ikirarin cewa suna daukar matakai da nufin murkushe ƴan bindiga, tare da samar da kariya ga dalibai.

A ɗaya ɓangaren kuma bikin na bana wanda UNESCO kan jagoranta ya koka da yadda miliyoyin yara kan gaza samun ingantaccen ilimi a kasashen da ke fama da rikici, kama daga ta’addanci da rikicin kabilanci da ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan