‘Yar Marigayi Sheikh Ja’afar Ta Zama Shugabar Mata Ta Izala

394

‘Yar marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, Zainab Ja’afar Mahmud Adam ta zama shugabar mata ta Sashin Matan Sunna (Nisau Sunnah) na Ƙungiyar Izalatul Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah, JIBWIS da aka fi sani da Izala.

Da take gabatar da jawabin karɓar wannan muƙami bayan naɗin nata Nisau Malama Zainab ta gode wa Allah da ya ba ta wannan muƙami.

“Na gode da ba ni wannan matsayi ba don mun fi kowa ba, amma sai don amincewa da aka yi da mu da nufin cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu. Kuma muna fata Allah zai ba mu dama mu fita kunyarku, kuma muna fata ya ba mu ikon yin daidai.

“Saboda haka, muna buƙatar jagorancin shugabanni ta fannoni daban-daban- ta ɓangaren yi mana addu’a a matsayin iyayemu da kuma ba mu umarni”, in ji Malama Zainab.

Ta kuma jaddada muhimmancin shigar da mata a wuraren da ake buƙatar ci gaban al’umma, tana mai ƙarawa da cewa ana buƙatar gudunmawar mata a wajen kawo ci gaba.

Idan dai za a iya tunawa, an kashe marigayi Sheikh Ja’afar ne a 2007 a lokacin da yake limancin sallar Asuba a jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan