Ƴan Najeriya na cigaba da rige – rigen komawa amfani da manhajar Telegram

233

Kwana ɗaya da shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da WhatsApp da Instagram su ka dawo aiki bayan matsalar daukewa da aka samu wadda ta kai tsawon kusan sa’a shida in ji kamfanin Facebook, ƴan Najeriya na yin hijira daga manhajar WhatsApp zuwa manhajar sadarwa ta Telegram.

A jiya ne miliyoyin al’umma su ka fuskanci matsalar shiga shafukan guda uku mallakin Facebook a kan wayoyin hannu da intanet.

Sai dai kamfanin ya ɗora alhakin matsalar a kan wata tangarda da ya fuskanta daga ɓangarensa.

Lamarin ya shafi manyan al’ummar manyan ƙasashen duniya da ma masu tasowa ciki har da Najeriya.

Wannan dalilin ne ya sanya shafukan sadarwar da dama na intanet da suka hada da Reddit da Twitter, su ka dinga yin shagube a kan matsalar ta Facebook da sauran shafukan mallakarsa abin da ya jawo martani daga shafukan da matsalar ta shafa.

Sai dai su kuma ƴan Najeriya tuni su ka ɗauki matakin inda hagu taƙi a koma dama domin mafi yawan masu amfani da manhajar WhatsApp ɗin sun mayar da hankalinsu ne kan barin Whatsapp din tare da komawa Telegram domin kaucewa fuskantar matsala.

Yadda ake rige – rigen komawa amfani da shafin sadarwa na Telegram

A cikin watan Janairun shekarar nan ne dai shafin sadarwa na Telegram ya fitar da wata sanarwa cewa yawan masu amfani da shi sun haura miliyan 500, kuma yana ƙara samun jama’a daga masu ficewa daga WhatsApp.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan