Abin Kunya Ne Yadda Limaman Cocin Katolika Ke Lalata Da Yara— Pope Francis

368

Abin Kunya Ne Yadda Limaman Cocin Katolika Ke Lalata Da Yara— Pape Francis

Pope Francis, Shugaban Kiristoci na Duniya ya ce abin kunya ne yadda ake samun malaman Cocin Katolika a Faransa da cin zarafin yara ta hanyar lalata.

Pope Francis ya bayyana haka ne ranar Laraba a gaban wani taron jama’a a Fadar Batikan.

Wani kwamitin bincike da aka kafa ya fitar da rahoto a ranar Talata cewa an ci zarafin yara da matasa aƙalla 216,000 a Cocin Katolika ta Faransa tun daga shekarun 1950 zuwa yanzu.

Ana jin cewa yaran da lalatar ta shafa za su iya kai 330,000, idan aka haɗa da cibiyoyin dake ƙarƙashin cocin.

“Yaran suna da yawan gaske”, in ji Pope.

Ya bayyana “baƙin ciki da raɗaɗi da yaran da abin ya shafa ke shiga… kuma abin kunya ne a gare ni, abin kunya ne a gare mu duka”.

Pope Francis ya yi kira ga Bishop-Bishop da jagororin majami’u da su yi duk mai yiwuwa don ganin cewa hakan bai sake faruwa ba “don Cocin ta zama wajen aminci ga kowa”.

Wani taron Bishop-Bishop a ranar Laraba ya tabbatar da cewa za a ba yaran da cin zarafin ya shafa tallafin kuɗi.

“Ba za ka iya gyara abin da ba zai gyaru ba”, Archbishop Eric de Moulins-Beaufort, Shugaban Taron Bishop-Bishop na Faransa ya shaida wa kafar France Info haka.

Pope Francis yi kira ga Cocin Katolika da ta kula da yaran kuma ta ɗauki alhakin faruwar haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan