Ɗalibar BUK da Akayi Garkuwa da ita ta Bayyana a Unguwar Sabon Gari.

811

Bayan shafe kusan awanni 48 da zargin yin garkuwa da ɗalibar Jami’ar Bayero Kano, wacce ke karantar kimiyyar tsirrai mai suna Sakina Bello, ta bayyana a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano.

Wani ɗan uwa ga ɗalibar ya shaida wa Jaridar Sahelian Times, cewa ko biyar ba a bayar ba kafin ɗalibar ta kuɓuta

Ya kuma bayya cewa ” ta kira ‘yan gida ta bayyana musu cewa ta kuɓuta daga hannun wanda su ka yi garkuwa da ita”

To sai dai mun so jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Kano, DSP Abdullahi kiyawa, amma harzuwa kammala wannan rahoto ba mu same shi ba, amma da zarar ya magantu zamu sanar da ku.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan