Tashar nishadantarwa Africa Magic mallakar rukunin kamfanin MultiChoice na duba yiwuwar shirya fim kan rayuwar matar shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari.
Shugabar kamfanin na yammacin Afrika, Busola Tejumola, ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta ke jawabi a taron kwana biyu da Africa Magic ta shirya na baje koli a jihar Kano, wanda aka kammala jiya Talata.
A takardar da MultiChoice ta fitar, taron da ta shirya an samu ya hade da taron shekara- shekara na kungiyar watsa labarai na Najeriya, BON ya samar da dama ga furodusoshi wurin mu’amala kai tsaye da Africa Magic domin samun damar tallatawa da siyar da hajojinsu.
Taron wanda ya samu halartar sama da furodusoshi dari biyu daga arewacin Najeriya, na son samar da hanyar samun riba da nasara ga dukkan masu ruwa da tsaki, a cewar Tejumola.
BBC Hausa