Cibiyar Koyon Sana’a Ta Ɗangote Na Dab Da Fara Aiki— Ganduje

410

Gwamnatin Jihar Kano ta ce kawo yanzu ta kashe naira biliyan N5.5 a wajen gina Cibiyar Koyon Sana’a ta Zamani wadda ta sa wa sunan hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Aliko Dangote.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka ranar Laraba a Kano.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a yayin da yake zagayawa da wakilan Broadcasting Organization of Nigeria, BON a cikin cibiyar.

Ya ce Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo zai ƙaddamar da cibiyar a watan Nuwamba.

Gwamnan ya ce cibiyar za ta fara aiki da mutane 500 da za a horar.

Ya ce kayan aiki na zamani da gwamnatin Kano ta siyo daga Turai da za a yi amfani da su a cibiyar za su zo Kano nan da ƙarshen Oktoba.

Gwamna Ganduje ya ce hukumar kula da Makarantun Koyon Sana’a ta ziyarci cibiyar don tantance kwasa-kwasanta.

“Don mayar da cibiyar cikakkiyar ‘yar Najeriya, kaso 60 cikin ɗari na gurbin karatu na ‘yan Kano ne ba tare da kula da matsayin addini ko na zamantakewa ba.

“Sauran kaso 40 ɗin za a raba shi tsakanin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT”, in ji shi.

Ya ce tuni an ɗauki masu kula da kayayyaki da malamai da za su koyar, kuma rukunin farko na ɗalibai za su fara karɓar horo a mako na biyu na Oktoba.

Wakilan sun kuma duba sauran ayyuka da suka haɗa da aikin gadar sama a Kasuwar Kantin Kwari da hanyoyin Madobi, Dangi da Barikin Bokabo da Cibiyar Kula da Masu Cutar Kansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan