Ciyo Bashi Ne Ya Sa Muka Iya Fita Daga Komaɗar Tattalin Arziƙi— Buhari

286

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ta yi amfani da bashin da ta ciyo don fita daga komaɗar tattalin arziƙi da ta shiga har sau biyu.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya gabatar da kasafin kuɗin 2022 a gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa ranar Alhamis.

Najeriya ta yi amfani da bashi “don fita daga komaɗar tattalin arziƙi da ta shiga har sau biyu”.

Ya jaddada cewa da Najeriya ba ta ciwo basussuka ba da ba ta iya fita daga komaɗar tattalin arziƙi ba.

“Kamar yadda kuka sani, mun samu komaɗar tattalin arziƙi har sau biyu a lokacin wannan gwamnatin tamu. A duka biyun, dole muka yi abin da za mu iya fita daga ciki, abin da ya tilasta ƙarin ciyo bashi. Abu ne mai wahala mu iya fita daga komaɗar tattalin arziƙin ba don ƙarin cin bashin ba”, in ji Shugaba Buhari.

Duk da wannan ɗimbin bashi, gwamnatin Buhari za ta ƙara ciyo naira tiriliyan N5.01 don aiwatar da kasafin kuɗin 2022.

A cewar Hukumar Kula da Basussuka ta Ƙasa, adadin kuɗin da ake bin Najeriya a watan Disamba, 2020 ya kai tiriliyan N32.915.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan