Fitaccen sha’irin Manzon Allah ɗin nan ɗan jihar Kano, Hafiz Abdallah ya jagoranci share titunan jihar Kano a wani yanayi na nuna murna da kamawar watan Rabi’ul Auwal, watan da aka haifi Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rubutu da Ambato TV ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba.
“A ci gaba da maraba da watan da aka haifi MAFI ALKHAIRIN duniya da lahira, ANNABI MUHAMMAD S.A.W, a yau Laraba Shugaban Cibiyar Ambato (Dr). Muhammad Hafiz Abdallah ya jagoranci tawagar Ambato wajen tsabtace tituna da lokunan birnin Kano da kewaye don nuna farin cikinmu da watan da HASKEN ALLAH ya bayyana a duniya”, kamar yadda rubutun ya bayyana.
Watan Rabi’ul Auwal dai shi ne wata na uku a jerin watannin Musulunci, kuma shi ne watan da aka haifi Fiyayyen Halitta.
Dubban al’ummar Musulmi sukan yi murna duk shekara idan watan ya zagayo don nuna godiya ga Allah bisa samuwar Fiyayyen Halittar.