Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar Najeriya ba ta damu da asalin duk wanda zai zama shugaban ƙasa ba, kuma hakan ma bai taɓa zama matsala a gare ta ba.
Atiku ya bayyana haka ne a Abuja a yayin taron tattaunawa na Kwamitin Zartawa na Jam’iyyar PDP, NEC, ranar Alhamis.
“Asalin shugaban ƙasa bai taɓa zama matsalar Najeriya ba kuma zan iya kawo misalai. Kuma ba shi ne mafita ba.
“Ba wani abu kamar a ce shugaba ya fito daga Kudancin Najeriya, ko kuma shugaba ya fito daga Arewacin Najeriya. Shugaban ƙasa ɗaya ne, shugaba daga Najeriya don ‘yan Najeriya wanda ‘yan Najeriya suka zaɓa”, in ji Atiku.
Ya yi kira da a yi adalci wajen fitar da yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP zai fito a 2023.
Ya ce matakin da za a ɗauka a taron na Abuja shi zai nuna ko PDP za ta iya dawowa kan mulki a 2023 ko kuma a’a.
Atiku ya ce PDP tana da ikon ta yanke hukunci bisa al’amuran da suka shafe ta, haka su ma al’ummar Najeriya suna da ikon su zaɓi wanda zai shugabance su.
“Ina magana game da shigo da kowa da kowa, zan so in ga matasa da yawa mata a taron NEC na gaba”, ya ƙara da haka.