MARTANI: Mayaƙan Boko Haram 87 Ƙungiyar ISWAP ta Hallaka a Borno

285

Ƙungiyar ISWAP ta kai hari kan mayaƙan Boko Haram a wani lamari mai kama da ɗaukar fansa a yankin Tafkin Chadi.

Hakan na zuwa ne kwana biyar bayan da wasu mayaƙan Boko Haram suka kashe mayaƙan ISWAP 24 a Tsaunukan Mandara da Gaba a garin Gwoza na jihar Borno, kamar yadda kafar yaɗa labaran PRNigeria ta ruwaito.

Mayaƙan ISWAP ɗin sun kai harin ne sansanin kwamandan Boko Haram Bakoura Modou a yankin Tafkin Chadin a jiya. Ku karanta: Miƙa wuyan da ƴan Boko Haram ke yi na jefa jihar Borno cikin mawuyacin hali – Zulum

PRNigeria ta ce mayaƙan ISWAP ɗin sun far wa sansanin Boko Haram ɗin ne a cikin wasu kwale-kwlae masu tsananin gudu har 50.

“An kashe fiye da mayaƙan ISWAP 87 a faɗan, a cewar kafar PRNigeria.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan