Me ya sa ƴan Najeriya ba sa ɗokin kasafin kuɗin 2022 da Buhari ya gabatar?

350

A yau Alhamis Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2022 a gaban zaman haɗin gwiwa na ‘yan majalisun tarayyar ƙasar nan.

Shugaba Buhari ya ce kasafin na shekarar 2022, zai mayar da hankali ne wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta soma kuma ƙudurin kasafin kuɗin na 2022, wanda ya kai naira tirliyan 16 da ɗigo 39.

Kuɗin dai, ƙari ne a kan naira tiriliyan 13.98 na kasafin kuɗin shekara 2021.

Haka kuma gwamnatin shugaba Buhari ta bayyana shirinta na ciyo karin bashi don samun karin kudi har Naira tiliyan 6 da biliyan 258, da zata cike gibin da za a samu a kasafin kudin da shugaban zai gabatar na shekarar 2022.

Daga cikin kudin da shugaban kasar ya gabatar a kasafin kudin na 2022, har da muhimman bangarorin da za a warewa kudade kamar hukumar zaben kasar, wadda ake sa ran tanadar mata karin naira biliyan 100, don shirin kasar na tunkarar babban zaben 2023.

A yayin gabatar da kasafin kudin dai, shugaban na Najeriya ya sanar da ajiye gangar man fetir daya a kan farashin dala 57, da kuma hako man fetir ganga kusan miliyan biyu a kullum.

Shugaba Muhammadu Buhari ke nan a lokacin da ya ke gabatarwa da majalisar ƙasa kasafin kudin shekarar 2022

Sai kuma canjin dala daya a kan Naira 410 da silai 15, da kuma hasashen samun kudin shiga Naira tiriliyan 3 da digo 15 daga bangaren man fetur.

Sai dai gabatar da kasafin kudin na bana ya zo da sabon salo domin mafi yawan yan Najeriya sun nuna halin ko in kula da batun kasafin kudin, ba kamar a lokutan baya ba da su kan cika kafafen sadarwa na zamani da hotunan shugaba Muhammadu Buharin.

Sai dai Malam Ali Sabo wanda shi ne babban jami’i mai kula da hulɗa da jama’a a cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato Centre for Information Technology and Development CITAD da ke birnin Kano, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sanya ƴan Najeriya ba sa murna ko doki da kasafin kuɗin shi ne tuni su ka dawo daga rakiyar gwamnatin APC da shugaba Buhari.


Ali Sabo ya ce “Maganar Allah babban dalilin da ya sa al’umma basa murna ko damuwa da wannan kasafin kudi da shugaba Muhammad Buhari ya gabatar a gaban kwamatin zartarwa na ƙasar nan dalilai ne masu yawa. Na farko dai in mu ka yi duba da shi kansa kasafin kudin wanda aka yi da ya kai Naira Tirilayan sha shida duk mai ilimi zai fahimci cewa wannan wani abu ne da bature yake kira “unrealistic budget’ wato ma’ana ba abu bane mai yiyuwa”

Sannan kuma al’umma da yawa sun daɗe da dawowa daga rakiyar wannan gwamnati musamman akan al’amura da suka shafi su kansu al’ummar, saboda an sha ɗanɗana musu zuma a baki a baya amma sai daga ƙarshe su fahimci ashe maɗaci ne”

“Gwamnati tasha yin alƙawarruka dan inganta rayuwar talakawa amma ba ta cikawa. To ina tsammami waɗannan dama wasu dalilai da ban zayyana a nan ba suna da alaƙa da abinda ya sa al’umma ba sa wani batu akan wannan kasafin kudin”

A Najeriya dai karshe da farkon kowacce shekara dai kan kasance wani lokaci na bayyana dubban miliyoyin nairori a matsayin kasafin kudi na gudanar da ayyukkan gwamnati, kasafin kudin da bisa al’ada ba kasafai ake aiwatar dashi ba a kammale

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan