Shahararren dan wasan kungiyar Manchester United, Marcus Rashford ya samu digirin digirgir na girmamawa daga jami’ar Manchester da ke Birtaniya.
Rashford shi ne mafi kankanta a shekaru a cikin tarihin wadanda suka taba karbar wannan digirin a jami’ar.
An bai wa Rashford, mai shekaru 23 wannan digirin na girmamawa ne domin Irin ayyukan da yake yi domin ganin cewa an kawo karshen talauci a tsakanin kananan yara.
A wurin taron karban digirin Rashford ya ce, “na ji dadin karban wannan digirin a gaban shahararru irinsu Sir Alex, amma lokaci ya yi da hukumomi ya kamata su shiga unguwanni kamar nawa, su ga wahalar da mutane ke ciki.”
Turawa Abokai