Yadda Jami’an Tsaro Suka Ceto Ɗaruruwan Mutane Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

232

Yadda Jami’an Tsaro Suka Ceto Kimanin Mutum 200 A Zamfara
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce ta ceto sama da mutum 180 waɗanda ‘yan fashin daji suka sace a ƙauyukansu, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan, Mohammed Shehu ya fitar, ya ce mutanen sun shafe makonni a hannun ‘yan fashin dajin.

An yi nasarar ceto mutanen ne bayan wani aikin nema da ceto da jami’an tsaro suka yi a dajin Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a jihar ta Zamfara, a cewar sanarwar.

Mista Shehu ya ce tuni aka miƙa mutanen hannun jami’an gwamnati domin kai su asibiti a duba lafiyarsu.

Jihar Zamfara dai ta daɗe tana fama da hare-haren ‘yan fashin daji, abin da har ya sa gwamnatin jihar ta katse harkokin sadarwa, a wani mataki na shawo kan wannan matsala ta tsaro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan