‘Yan Najeriya Kaɗan Ne Ke Biyan Haraji— Gwamnatin Tarayya

386

Muhammad Nami, Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya, FIRS, ya ce ‘yan Najeriya miliyan 41 ne kawai suke biyan haraji daga cikin mutane kimanin miliyan 200.

Mr Nami ya bayyana haka ne a yayin wani taron yi wa mutane jawabi game da kasafin kuɗin Najeriya na 2022 ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce duk da wannan adadin mutane miliyan 41 da suke biyan haraji, Najeriya tana samun ƙasa da abin da takwarorinta a nahiyar Afirka ke samu daga hannun jama’a.

“Idan kuka kwatanta da Afirka ta Kudu inda ake da yawan mutane miliyan 60, da masu biyan haraji mutum miliyan 4 kawai, jimillar harajin da mutane ke biya a Afrika ta Kudu ya kai tiriliyan N13.

“Yawan biloniyoyin da suke Legas kaɗai sun fi waɗanda suke Afirka ta Kudu gaba ɗaya, amma abin da muke samu a Legas a matsayin harajin da mutane ke biya ba shi da yawa.

“Saboda haka idan ba a biyan waɗannan haraji, babu yadda gwamnati za ta iya samar da kayayyakin more rayuwa don jin daɗin jama’a” in ji Mista Nami.

Ya ce jimillar harajin da aka tara zuwa 30 ga Satumba, wanda har yanzu Babban Bankin Najeriya, CBN, da Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS, ba su tantance ba shi ne tiriliyan 4.2, daga wannan adadi, wanda aka samu daga cikin man fetur shi ne kaso 22 wanda ya kai biliyan N950, jimillar harajin da aka samu ba daga mai ba shi ne tiriliyan N3.3.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan