Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin kasar a zaɓen shekarar 2019 Alhaji Atiku Abubakar ya yi wata ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Atiku Abubakar ya wallafa hotunan ganawar da ya yi da Sule Lamido a shafinsa na facebook a jiya a Juma’a.

Awanni kaɗan da fitar da hotunan ganawar da Atikun ya yi da Sule Lamido sai ga shi kuma Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad shi ma ya ziyarci Atiku Abubakar.

Wannan ganawar dai na zuwa ne mako ɗaya da kwamitin zartarwar jam’iyyar PDP na kasa ya amince da matakin da kwamitin raba mukamai a jam’iyyar ya yi na keɓewa yankin arewacin ƙasar nan kujerar shugaban jam’iyyar al’amarin da ya haifar da tada jijiyoyin wuya.