Muhuyi Ne Ya Ƙulla Kutungwila Har EFCC Ta Kama Gwaggo— Rahoto

746

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano na shirin maka tsohon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado a kotu bisa zargin sa da gabatar da bayanan ƙarya ga Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Idan dai za a iya tunawa, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci Muhuyi ya bayyana a gaban wani kwamitin bincike da ta kafa ranar 14 ga Yuni.

Sai dai Muhuyi ya gabatar da takardun da suke nuna yana da rashin lafiya, kuma ya buƙaci majalisar ta ba shi kwafin tuhumar da take yi masa, kuma ya buƙaci ƙarin lokaci kafin ya bayyana a gaban Majalisar.

A ranar 19 ga Yuni, Asibitin Ƙasa ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda ya ce takardun da Muhuyi ya gabatar ga Majalisar na bogi ne.

Hakan ne ya sa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta gayyaci Muhuyi don yi masa tambayoyi da kuma shirin maka shi a kotu

Sai dai bayan tuhumar, majiyoyin jami’an tsaro sun shaida wa jaridar Intanet, DAILY NIGERIAN, cewa ba a samu Muhuyi da laifi ba, kuma an dawo masa da fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye, inda aka nuna “ba a iya tabbatar da laifin gabatar da takardun bogi da haɗa baki don aikata laifi ba a kansa”.

Sai dai Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bai ji daɗin yadda ‘yan sanda suka gudanar da binciken ba, saboda haka ne ya dage kan cewa dole a maka Muhuyi a kotu.

Majiyoyi a Fadar Gwamnatin Jihar Kano su ce Gwamna Ganduje ya yi amannar cewa Muhuyi ne ya sa Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’anati, EFCC ta kama mai ɗakinsa.

“Gwamna ya ji haushin Muhuyi bisa gayyatar da EFCC ta yi wa mai ɗakinsa. Kowa ya yadda cewa Muhuyi ne ya sa a gayyace ta”, a cewar wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan