Shugaba kuma mamallakin jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana rasuwar shahararriyar mawaƙiyar Hausa nan, Hajiya Magajiya Ɗanbatta a matsayin babban rashi ga daukacin al’ummar Arewacin Nijeriya.
A cikin sakon ta’aziyyar da ke kunshe a cikin wata sanarwa da Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya Sanyawa hannu daga Faransa wadda aka aikowa da manema labarai, ta bayyana rasuwar Magajiya Danbatta a matsayin Babban Rashi ga al’umma baki ɗaya.
Ya ce La’akari da Gudummawar da Marigayiyar ta baiwa al’umma ta hanyar faɗakarwa ta hanyar Waƙe, Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta sanya wa ginin Koyar da harkokin Shari’a ta Jami’ar sunan Marigayiyar Hajiya Magajiya Ɗanbatta baya ga karrama ta bayan rasuwarta.
“Don girmama Marigayi Magajiya Ɗanbatta (Halima Malam Lasan) da gudunmawar da ta bayar a fannin ilimi, mun yanke shawarar karrama ta da digirin girmamawa bayan rasuwa.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “mun yi shirin karrama ta a lokacin tana da rai amma, ta mutu kafin Lokacin taron.”

Wannan, sanarwar ta ce, baya ga sanyawa Sashen Shari’a suna. Manazarta sun ce “Za mu yi rashin barkwancinta da shahararrun waƙoƙinta”.
Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda shi ne a matsayin Shugaban Kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu a Afirka ya bayyana rashin Magajiya Ɗanbatta Makoda a matsayin abin takaici. Inda Sanarwar tace a madadin iyalansa da ɗaukakin Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, yana mika ta’aziyar su ga iyalai da abokan arzikin marigayiyar da ma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Fitacciyar mawaƙiyar Hausa, Halima Malam Lasan, wacce aka fi sani da Magajiya Ɗanbatta ta rasu tana da shekaru 85 bayan gajeruwar jinya a babban asibitin Ɗanbatta a ranar Juma’a 8 ga Oktoba 2021.
Guda daga cikin waƙoƙin ta ta bada gudummawa sosai wajen sanya yin rijistar yara sama da 3,000 a makarantu a farkon Shekarar 1970.
Idan za a iya tunawa a shekarar da ta gabata, Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ta haɗa kai da wasu mutane don tara kudaɗe don tallafawa Marigayiya Mawaƙiyar wanda ya kai ga gina Gida da samar mata da kayan abinci.

Rahoton ya ce marigayi Dambatta ta makance saboda mawuyacin halin rayuwa data shiga wanda ya kai ta ga yin bara.
Farfesa Gwarzo ya kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki da Ya baiwa Marigayiya Aljannah Firdausi da iyalinta juriyar jure rashinta.
Ni muhammad Abdullahi Gama
Ina Mika sakon ta a ziyya ta ga iyalan marigayi magajiya Dan batta Ina adduar Allah yagafarta mata yasa aljannah makoma
Muhammad Abdullahi Gama