Ƴan Shara A kano Kusan wata 4 babu albashi
Masu sadaukar da kansu a bakin titunan birnin kano domin tsaftace birnin suna cikin ruɗani tun bayan da gwamnatin kano ta ce ta cefanar da hukumar REMASAB ta koma hannun wani kamfani mai suna CAPE GATE.
Kusan wata huɗu kenan har zuwa yanzu wannan kamfani bai biya ma’aikatan albashi ba.

Abin tausayin ma shi ne zaka ga ma’aikatan akwai tsofaffin da basu tsaya barace-barace ba suka zo suke wannan aikin domin samun ɗan abin da ba’a rasa ba. Amma wai aka barsu cikin wannan yanayin.
Tuni aka sa ma’aikatan sharar zuwa banki don buɗe asusu wanda aka ce yanzu ta asusun za’a ke biyansu albashi.

Rahoton da muke samu kawo yanzu dai ya nuna cewa kusan gaba ɗaya ma’aikatan sharar sun buɗe sabon asusun da aka buƙaci su yi tun watan da ya kamata, amma shiru kake ji har yau ga shi 10 ga sabon wata.
To amma abin tambayar shi ne daga ina ainihin matsalar ta ke?
Bayan karɓe iko da REMASAB sabon kamfanin na CAPE GATE ya ce zasu fito da sabon tsarin ƙarin albashi ga ma’aikatan, amma dai shi ma wannan shiru kake ji.

Su dai ma’aikatan yanzu ba ma ta ƙarin albashi suke ba, burinsu a biya su hakkinsu idan yaso daga baya sai ayi maganar ƙarin albashin.
A tausayawa Talaka