Asibitin Malam Aminu Kano Zai Yi Wa Masu Larurar Tsagewar Leɓe Aiki Kyauta

361

Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH, ya ce zai yi wa marasa lafiya masu fama da larurar tsagewar leɓe aiki kyauta.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’ar Huɗɗa da Jama’a ta Asibitin, Hauwa Muhammed ta fitar ranar Lahadi.

Asibitin ya ce tawagar likitocinsa za ta yi wannan aiki ne ranar Asabar, 16 ga Oktoba, 2021.

Haka kuma, manyan mutane da suke fama da wannan larura su ma za a yi musu aikin kyauta.

Sanarwar ta ce asibitin ya fara yin irin wannan aikin na kyauta ne tun a 2018, kimanin mutum 100 suka ci gajiya.

Sanarwar ta ƙara da cewa likitocin haƙora da na fuska na asibitin su ne suka gudanar da aikin.

Tawagar likitoci kimanin 30 ne za su gudanar da aikin.

Asibitin ya yi kira ga jama’a da su yaɗa wannan sanarwa don kowa ya samu ya amfana.

Tawagar likitocin ta gode wa cibiyar Smile Train Initiative bisa yadda ta haɗa kai da asibitin don a taimaka wa marasa lafiyar.

Sun yi kira ga sauran jama’a da ƙungiyoyi da su yi koyi da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan