Tsohon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce faya-fayan bidiyon da aka fitar na dala da suka nuna Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karɓar cin hanci sun sa masu zuba jari sun bar jihar Kano.
Muhuyi ya bayyana haka ne a wani shirin tattaunawa da Freedom Radio, Kano ta yi da shi ranar Lahadi.
Idan dai za a iya tunawa, a 2018 ne jaridar Intanet, Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayan bidiyo, inda aka nuna Gwamna Ganduje yana karɓar cin hanci na dalar Amurka daga hannun ‘yan kwangila.
Sakamakon haka ne Gwamna Ganduje ya maka jaridar da mawallafinta, Jafaar Jafaar a kotu bisa zargin ɓata masa suna.
Sai dai Gwamna Ganduje ya janye ƙarar a Yuni, 2021 a lokacin da kotun ta buƙace shi ya biya Jaafar tarar N800,000 ga Daily Nigerian da Jaafar Jaafar a matsayin tara ta ɓata masa lokaci.
Har yanzu dai Gwamna Ganduje bai biya tarar ba, kuma ya ƙara shigar da wata ƙarar.
Muhuyi ya bayyana a cikin shirin cewa tun lokacin da aka wallafa faya-fayan bidiyo, masu zuba jari sun daina tallafa wa jihar Kano da kuɗaɗe.
“Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe daga wasu game da rashin daidaito a cibiyar kula da masu kansa kuma muka fara bincike game da batun. A lokacin binciken, an yi zargin cewa an cire miliyan N700 daga lalitar gwamnati aka ajiye su a wani banki a Wudil”, in ji Muhuyi.
A cewar Muhuyi, zargin ya nuna wani jigo ne a gwamnatin Kano ya fitar da kuɗaɗen.
Ya ƙara da cewa an kuma samu wani zargin badaƙala game da tallafin karatu na ɗaliban Kano masu karatu a Misra, ya ce har lokacin da aka dakatar da shi ana wannann bincike
Lokacin da jaridar Intanet, Solacebase ta tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai game da wannan zargi mai cewa masu zuba jari na gudun jihar Kano, ya ce ba shi da masaniyar haka, yana mai cewa ma’aikatarsa ba ta mu’amala da masu bada tallafin kuɗaɗe.
“Za ka iya tuntuɓar MDAs da suke mu’amala da masu bada tallafin kuɗaɗe ko kuma ka yi bincikenka don tabbatar da wannan zargi cewa masu zuba jari sun guji jihar Kano”, in ji Muhammad.