Labaran Bogi Su Ne Manyan Matsalolin Najeriya

297

Nuhu Ribadu, tsohon Shugaban Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’anati, EFCC, ya yi zargin cewa cewa yawancin matsalolin Najeriya suna da nasaba da yaɗa labaran ƙarya.

Ribadu ya bayyana haka ne ranar Lahadi a yayin wani taron manema labarai a Abuja.

Tsohon Shugaban na EFCC yana mayar da martani ga wasu rahotanni da suke cewa ya zargi wasu jigajjigan jami’an Gwamnatin Tarayya da ɗaukar nauyin ta’adanci a ƙasar nan.

Mista Ribadu ya ce lokaci ya yi da zai yi bayani game da batun, wanda ya daɗe da bazuwa.

“Yuni 2019 shi ne lokacin da na san haka kuma na musanta hakan sosai, na ce ƙage ne kuma babu ƙanshin gaskiya.

“Shirme ne kawai cike da kurakurai a nahawun da ƙage-ƙage.

“Na mayar da martani mai ƙarfi bayan haka, bai tsaya ba, aka tilasta min dole in fitar da sanarwa ta musantawa”, in ji Ribadu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan