Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani mutum mai suna Aminu Inuwa, hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samun sa da laifin kashe matarsa mai suna Safara’u Mamman.
Aminu, wanda kotu ba ta bayyana shekarunsa, ba mazaunin unguwar Gwazaye ne dake ƙaramar hukumar Gwaje ta jihar Kano.
Mai Shari’a Usman Na’abba ya tabbatar da cewa masu ƙara sun gamsar da kotu game da ƙarar da suka shigar.
Tun da farko, lauya mai gabatar da ƙara, Lamiɗo Sorondinki, ya faɗa wa kotun cewa Aminu ya aikata wannan aika-aika ne ranar 2 ga Afrilu, 2019 a unguwar ta Gwazaye.
Lamiɗo ya ce mai laifin ya caka wa matar tasa wuƙa ne a maƙogwaro a lokacin da suka yi wata sa-in-sa, ya kuma binne ta a cikin wani kangon ɗaki a gidansa.
Lauya mai gabatar da ƙarar ya kawo shaidu uku da hujjoji shida don tabbatar da iƙirarinsa.
Ya ce wannan laifi ya saɓa da Sashi na 221 (a) na dokokin Penal Code.
Sai dai mai laifin ya musanta aikata haka.
Lauya mai bada kariya ya gabatar da shaida ɗaya mai Mustafa Idris.