Masallatai A Jamus Sun Samu Damar Yin Kiran Salla A Fili

868

Masallatai a Jamus sun samu izinin yin kiran salla a fili a ranakun Juma’a da rana, bayan wata yarjejeniya da aka samu tsakanin birnin Kolon da al’ummar Musulmi don sauƙaƙa takunkumi, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Dukkan masallatai 35 da suke birnin Kolon a yanzu sun samu damar kiran salla a fili daga ƙarfe 12:00 na ranar kowace Juma’a zuwa 3:00 na yamma a ƙarƙashin wata yarjejeniya ta shekara biyu.

Wannan dama dai ta haɗa da Babban Masallacin Kolon, wanda aka buɗe a 2018 bayan an sha samun rikici.

“Ƙyale ladani ya yi kiran salla alamar girmamawa ne”, Magajiyar Birnin Kolon, Henriette Reker ta wallafa haka a Twitter.

Kiran salla zai riƙa haɗuwa da ƙaraurawar cocin Kasedral– babbar cocin Gothic a Turai.

“Hakan yana nuna ana amsar kowa da yake zaune a Kolon”, in ji ta.

A lokacin da ake cece-ku-ce game da ginin Babban Masallacin Kolon, masu ginin sun tabbatar wa da jama’a cewa ba za a riƙa kiran salla sau biyar ba, kamar yadda ake yi a ƙasashen Musulmi.

Birnin Kolon ya ce dole masallatan da suke so su riƙa kiran salla ranar Juma’a su bi dokar rage ƙarar lasifikokinsu, kuma dole su sanar da maƙobtansu kafin su kira sallar.

Akwai Musulmi kimanin miliyan 4.5 a Jamus.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan