Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan gaba kaɗan Najeriya za ta fara ƙera makamai domin sauƙaƙe yaƙi da matsalolin tsaro da take fama da su, a cewar wani rahoto na BBC Hausa.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin taron da yake jagoranta na kwana biyu a Fadar Shugaban Ƙasa kan ayyukan da gwamnatinsa ke gudanarwa a ma’aikatu daban-daban, kamar yadda rahoton na BBC Hausa ya ce.
Shugaban Najeriyar ya ce tuni aka bai wa Ma’aikatar Tsaro umarnin ƙirƙiro wata masana’anta domin ƙera makamai a cikin gida da zummar biya wa rundunar sojan ƙasar buƙatunta.
Ya ƙara da cewa samar da masana’antar makaman a Najeriya zai bayar da damar rage dogaro da ƙasar ke yi kan ƙasashen waje.
Za a ƙaddamar da shirin ne a ƙarƙashin Sashen Masana’antu na Rundunar Sojan Najeriya mai laƙabin Defence Industries Corporation of Nigeria (DICON), a cewarsa.
Ya zuwa yanzu Najeriya ta yi nasarar ƙera jiragen ruwa na soja da wasu ƙananan tankokin yaƙi waɗanda shugaban ya ƙaddamar a ƙarshen 2020.
A Yulin da ya gabata ne kuma Najeriya ta karɓi jiragen yaƙi da ta sayo daga Amurka na A-29 Super Tucano, waɗanda Buhari ya ce “ana amfani da su wajen bayar da horo da kai farmaki da tattara bayanai ga dakarun Najeriya”.