2023: Abdulmumin Jibrin Kofa ya fara shirin haɗa kan matasan Najeriya mai laƙabin G – 23

874

A dai-dai lokacin da manyan zaɓukan Najeriya da za a yi a shekarar 2023 ke ƙara matsowa tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, Abdulmumin Jibrin Kofa, tare da wasu fitattun matasa ƴan Najeriya na shirye-shiryen yin gangamin matasa da za su taka rawa a zaɓen da ke tafe mai taken Group 23 (G -23).

Abdulmumin Jibrin Kofa ya sanar da wannan shiri na su ne a jiya Talata, inda ya tabbatar da cewa wannan gangamin na cikin ƙoƙarin dawo da karsashi da martabar jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023.

Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa

“Shiri ne da mu ka yi masa cikakken tsari da ya haɗa da zaƙaƙurrarun matasan Najeriya tun daga matakin rumfar zaɓe da ke faɗin ƙasar nan. Kuma babbar manufar G – 23 shi ne samar da gangamin siyasar da babu irinsa a Najeriya, inda zai taka rawa a zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ta hanyar bayar da cikakken goyon baya ga ɗan takarar shugabancin Najeriya”

Abdulmumin Jibrin wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilan Najeriya na da tarihin siyasa mai karfin gaske, domin an ga yadda ya taka rawa a lokacin yaƙin neman zaɓen kakakin majalisar wakilai na ƙasa a shekarar 2015 da kuma 2019, ya ce matasa na da rawar takawa a harkokin da su ka shafi cigaban ƙasa dan haka abu ne mai kyau a samar musu da runduna mai ƙarfi.

Abdulmumin Jibrin Kofa lokacin da ya yi ganawa da shugaba Muhammadu Buhari

“Tun lokacin da na shiga siyasa bani da burin da ya wuce ganin an samar da wani tsari mai karfin gaske da zai haɗa kan matasan Najeriya guri guda ta yadda za su zama wakilan sa kai a rumfunan zaɓen da ke faɗin Najeriya”

“Wannan shirin na mu ba dare ɗaya mu ka yi shi ba, mun ɗauki tsahon shekaru wajen ganin ya tabbata domin ita siyasa batu a ke na jama’a, kuma muna da al’ummar, abu daya kawai mu ke buƙata shi ne samar musu da tsafatacciyar hanyar da za ta kai su ga tudun mun tsira”

Abdulmumin Jibrin Kofa yana yiwa ɗimbin magoya bayansa jawabi a wani taro na siyasa

“kuma zamu yi amfani da fasahar sadarwar zamani a wannan shiri namu ta yadda za ta haɗamu da mutanenmu da su ke sassan kasar nan a cikin ƙanƙanin lokaci”

“Babban burina da fatana shi ne ganin wannan gangami ko haɗakar matasan nan ta zama mafi ƙarfi da girma da kuma tasiri da za ta taka rawa a zaɓen shekarar 2023 da ke tafe da bayansa ” In ji Abdulmumin Jibrin Kofa.

Abdulmumin Jibrin Kofa tare da ɗaruruwan magoya bayansa

A ƙarshe tsohon ɗan majalisar wanda shi ne babban daraktan cigaban harkokin kasuwanci na hukumar kula da gidaje ta tarayya (FHA), ya bayyana cewa nan gaba kaɗan za su sanar da ranar da za a ƙaddamar da wannan gangami a hukumance kuma birnin tarayya Abuja ne zai zama shalkwatar wannan gangamin matasan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan