Mulki da jagorancin al’umma na Malamai ne ba na Ƴan Siyasa ba – Farfesa Auwal Magashi

  499

  Allah maɗaukakin Sarki shi ne ya zaɓi Annabawa da Manzanni ya turo su domin su jagoranci al’umma, su saita ta a kan abin da zai gadarwa al’umma arzikin duniya da lakhira. Magadan Annabawa da Manzanni sune malamai, saboda haka sune suka fi cancantar su jagorancemu ba ‘yan siyasa ba. Lallai sake zaɓen ‘yan siyasar yau, domin su jagoranci alummarmu, cin amanar Allah da Manzonsa da alumma ne baki ɗaya.

  Hakika ‘Yan siyasar da muka zaɓa mun yi fatan za su riƙe amanar Allah da Manzonsa da nauyin da Allah ya ɗora musu, yanzu mun fahimci sun faɗi wanwar, sun ballagazar da amanar Allah da ke kansu da amanar Manzon Allah SAW da amanar al’umma baki ɗaya. Ina kiran kaina da su da mu ji tsoron Allah, ‘yansiyasa kuma su gaggauta tuba izuwa ga Allah, su dawo da amanar da aka ɗora musu ga waɗanda suka cancanta. Waɗanda kawai sharia ta nuna siffofinsu ake bawa wakilci da shugabanci.

  ‘Yan siyasar mu na yanzu su koma gefe su gyara alaƙarsu da Allah su nemi al’umma ta yafe musu.

  Wanda duk ya gaza haka daga cikinsu, to lallai ya san yaci amanar Allah da Manzonsa da alumma (saboda rashin cancantarsa ga matsayin da yake kai), lallai ya saurari wulakanta a duniya da kunyata da kuma nadama a lakhira: “Innaha amanat wa innaha yaumul Qiyamati hizyun wa nadama, illa man ata bi haƙƙiha wa addallazi alaihi”. Alhadith

  Farfesa Auwal Ibrahim Magashi

  A kyakkyawan zatonmu muna da misalan malamai da suka cancanci su wakilcemu a matakan siyasa tun daga kan kansila har zuwa shugaban ƙasa. Saboda suna da waɗannan siffofi:

  1. Ƙwararrun Malamai ne masu koyarwa a kan mumbarai, majalisun ilmi da tarukan faɗakar da al’umma wajan gyarata da saita mata alƙibla.
  2. Suna da ido biyu (Ilmin Addini da na zamani), suna son Allah da manzonsa kuma alumma ce a gabansu, ba iyalansu kawai ba.
  3. Suna da siffofi uku na shugabanci (ƙarfi, ilmi da amana).
  4. Shekarun rayuwarsu 40-45 (na tsaka tsaki)

  Ina kira ga alumma da suke neman mafita a gurin Allah suke fatan zaman lafiya da nutsuwa a rayuwarsu ta duniya da su watsar da ‘yan siyasa su rungumi waɗannan malamai a matsayin wakilansu ko kuma masu zaƙulo wakilai da shugabanni- (Electoral College). Fatammu Allah ya kawo mana canji mafi alkhairi, Mu nisanci son zuciya wanda zai janyo mana fushin Allah.

  Madaukakin sarki yana gargaɗinmu da cewa: “Ya ku waɗanda kuka bada gaskiya! kada ku ci amanar Allah da amanar manzonsa da amanar da aka ɗora muku alhali kuma kuna sane…”. Quran

  Lallai Malamai su suka fi cancanta su ƙalubalanci Gwamnatin ‘yan siyasa amma cikin girmamawa da yi wa gwamnati fatan alkhairi da gyaruwa, ba da nufin tozartata da tunzura al’umma a kanta ba.

  Farfesa Magashi Auwal Ibrahim shi ne limamin masallacin juma’a na jami’ar kimiyya da fasaha da ke garin Wudil a jihar Kano.

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan