Wasu jigajjigan jam’iyyar APC a jihar Kano sun fara shirye-shiryen ƙwace jam’iyyar APCn daga hannun Gwamna Abdullahi Ganduje.
Sanataci uku ne suke a gaba-gaba wajen ƙwace jam’iyyar daga hannun Gwamna Ganduje da suka haɗa da Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau da Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin.
Rahotanni sun ce sanatocin sun yi taron ganawar ne a gidan tsohon Gwamna Shekarau ranar Talata da ta gabata.
Kodayake dai ba su bayyana maƙasudin ganawar tasu ba, amma wata majiya ta ce ganawar ba za ta rasa nasaba da yadda Gwamna Ganduje ya tsayar da Abdullahi Abbas ba a matsayin ɗan takarar shugabancin jam’iyyar APC a zaɓen shugabannin jam’iyyar na jiha da za a yi ranar 16 ga Oktoba, 2021.
Haka kuma, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni, kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, da kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado kuma Shugaban Kwamitin Bunƙasa Karkara na Majalisar Wakilai,Tijjani Joɓe da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaraye da Rogo, Haruna Dederi da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Gabasawa da Gezawa, Nasiru Auduwa.
Haka kuma an ga ɗan takarar shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano, Amadu Haruna Zago a wajen taron tattaunawar.
Rahotanni sun ce sanatocin ba sa jin daɗin yadda Gwamna Ganduje ke tafiyar da jam’iyyar APC, sun kuma yi zargin cewa Gwamnan ya mayar da Fadar Gwamnatin Kano ofishin APC.
Sun kuma yi zargin cewa Gwamna Ganduje yana tafiyar da APCn ne tare da wasu ‘yan tsirarun mutane a Kano.
Wani rahoto da hadimin Shugaban Ƙasa, Bashir Ahmad ya wallafa ranar ya ce a ranar Laraba da safe wasu jigajjigan APC daga Kano suka ziyarci Sakatariyar APC ta Ƙasa a Abuja, ziyarar da ake ganin tana alamta matsala a tsakar gidan jam’iyyar APCn ta Kano.
Wata majiyar kuma ta shaida wa jaridar Intanet, Solacebase, ca ranar Laraba cewa Gwamna Ganduje ya daɗe yana juya wa Shekaru baya.
Sai dai masana da’irar siyasar Kano sun ce idan banda marigayi Malam Aminu Kano, Shekarau ne ɗan siyasa mafi ƙarfin faɗa a-jin da za ta iya sauya siyasar Kano daga matakin unguwa har zuwa sama.