Shugabancin APC a Kano Malam Shekarau da jama’arsa na shirin ƙalubalantar Ganduje

695

Ƙasa da mako ɗaya da jami’yyar APC ta gudanar zaɓen shugabanni a matakin jihohi Sanatocin jihar guda 3 wato Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da kuma Sanata Barau Ibrahim Jibrin da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Tofa da kuma Rimin Gado sun yi wata ganawa ta musamman tare da mai neman shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago.

A ɗaya ɓangaren kuma mukarabban gwamnatin jihar Kano da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun nuna mubaya’ar su ga mai riƙon jam’iyyar Abdullahi Abbas Sanusi.

Abin tambayar shi ne ko gidan Malam Ibrahim Shekarau a cikin jam’iyyar APC a Kano ba sa tare da Abdullahi Abbas?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan