Za Mu Ba Manoma Rancen Biliyan N600 Don Bunƙasa Noma— Buhari

401

Mun Ware Wa Manoma Rancen Naira Biliyan N600— Buhari
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta ware wa manoman Najeriya naira biliyan N600 a wani shirinta mai suna Agro-Processing Productivity Enhancement and Livelihood Improvement Support project, APPEALS don bunƙasa aikin noma.

Shugaba Buhari ne ya bayyana haka ranar Laraba a Abuja a yayin Taron Nuna Amfanin Gona na 2021 na Ranar Abinci ta Duniya.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Ministan Aikin Noma da Raya Karkara, Dakta Mohammed Abubakar, ya ce ba zai yi sako-sako ba wajen ganin ya ɗora aikin noma a Najeriya akan kyakkyawar turba.

“Gwamnatin Tarayya, ta hanyar shirinta mai suna Agro-Processing Productivity Enhancement and Livelihood Improvement Support project, APPEALS, ta ware naira biliyan N600 a matsayin rance ga manoma a dukkan faɗin ƙasar nan.

“Aƙalla manoma miliyan 2.4 ne ake sa ran su amfana da rancen wanda babu ruwa ko kaɗan.

“Wannan abin kirki zai tallafa wa manoma a ƙasar nan wajen haɓaka nemansu” in ji Shugaba Buhari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan