Muna Tare Da Ganduje Ɗari Bisa Ɗari— Martanin Alhasan Doguwa Ga Shekarau

594

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, kuma ɗan majalisa mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa, Alhasan Ado Doguwa, ya caccaki tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin da wasu ‘yan majalisar huɗu bisa zargin cewa Gwamna Ganduje yana yin abin da ya ga dama da jam’iyyar APC.

A jiya ne sanatocin ƙarƙashin jagorancin Sanata Shekarau suka shigar da ƙorafi ga uwar jam’iyyar APC ta ƙasa, inda suka ce Gwamna Ganduje yana tafiyar da APCn ba tare da tafiya da kowa ba.

Suka ce Gwamna Ganduje ya mayar da su saniyar ware a harkokin jam’iyyar, duk da yadda suka taimaka sosai wajen nasarar ta.

A yau Alhamis ne kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta Kano suka yi wani taron ganawa gabanin zaɓen shugaban jam’iyyar da za a yi ranar 16 ga Oktoba, 2021.

“A iya sanin masu ruwa da tsaki, babu wata rigima a jam’iyyar nan”, a cewar Doguwa.

A cewarsa, ya yi mamakin me ya sa su Shekarau za su zargi Gwamna Ganduje da tafiyar da jam’iyyar ba tare da su ba,bayan a fili yake cewa Gwamnan yana tafiya da kowa da kowa.

Doguwa ya yi kira ga Gwamna Ganduje da ya hukunta su Shekarau, yana mai siffanta Gwamnan a matsayin mai tsananin haƙuri.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan