Rahotanni sun ce jami’an sojin Najeriya sun kashe wani ƙasurgimin ɗan ta’adda mai suna Alhaji Karki a lokacin da ya yi yunƙurin kai hari akan da wata rundunar soji.
Karki, wanda ya taɓa tuba amma ya koma ruwa, ya daɗe yana addabar ƙauyukan jihar Neja, ya jagoranci kashe-kashe, ƙone-ƙone da garkuwa da mutane.
Wasu majiyoyi sun ce Karki yana da runda mai ɗauke da makamai a ƙarƙashinsa.
“Alhaji Karki yana da ɗaruruwan ‘yan ta’adda a ƙarƙashinsa. Kuma yana da muggan makamai”, a cewar wata majiyar tsaro.
Tsohon Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Sani Usman, shi ma ya wallafa labarin kashe Karki da sojojin suka yi.
“Majoyoyin cikin gida sun tabbatar da kashe jagoran ‘yan ta’adda, Alhaji Karki a jihar Neja a lokacin da ya yi yunƙurin kai hari akan rundunar soji.
“Kashe wannan babban ɗan ta’adda ya kawo fata game yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda”, a cewar Sani a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Talata.