Aminu Alan Waƙa zai yi gagarumin Mauludi a Kano

804

Fitaccen mawaƙin nan Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waƙa kuma shugaban kamfanin Taskar Ala ya sanar da kudurinsa na shirya wani gagarumin Mauludi a ranar Lahadi 17 ga watan Oktobar nan a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Aminu Ala wanda shi ne ke riƙe da sarautar Ɗan Buran na Gobir da ke jihar Kebbi kuma shi ne Sarkin wakar Sarkin Dutse, ya sanar da ranar Mauludin ne a shafinsa na facebook.

Al’ummar Musulmai dai kan yi hidima a wannan lokaci, inda makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya mauludi ta hanyar ƙayata waje a gayyaci manyan baƙi a zo a bai wa ɗalibai karatu da waƙoƙi na yabon Annabi su zo su rinƙa yi.

Haka kuma da yawa daga cikin al’ummar Musulmai a faɗin duniya sun ɗauki ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal na kalandar Musulunci a matsayin ranar da aka haifi annabin a garin Makka da ke ƙasar Saudiyya.

Aminu Ladan Abubakar

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Talata 19 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW wato Maulidi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan