Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata, 19 ga Oktoba, 2021 a matsayin ranar hutu don murnar bikin Maulidin wannan shekarar don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (Sallal-lahu alaihi wa sallam).
Hakan dai ya fitone ta bakin Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya yi wannan sanarwar a madadin gwamnatin tarayya, ya na taya dukkan musulmin da ke cikin gida Nijeriya da na ƙasashen waje murnar bikin wannan shekarar.
Ya shawarci dukkan ‘yan Nijeriya da su sanya soyayya, haƙuri da juriya a rayuwar su kamar yadda wadannan su ne ɗabi’un Annabi Muhammadu (S.A.W), Inda ya ƙara da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
Ogbeni Aregbesola ya umarci ‘yan Nijeriya, musamman Musulmai, da su guji tashin hankali, rashin bin doka da sauran ayyukan da basu kamata ba.
Minista ya yi kira da a dakatar da duk wasu abubuwan da ke kawo rarrabuwar kawuna a faɗin ƙasar, ya kuma buƙaci dukkan ‘yan Nijeriya musamman matasa, da su rungumi ɗabi’un na gari inda yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na ƙoƙarin gina ƙasa don ci gaban al’ummar Nijeriya.