Yau kwanaki biyu ke nan da jiga-jigan jam’iyyar APC su ka yi zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere tare da yin gaban kansa wajen yanke hukunci a kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar a jihar Kano, sai dai har kawo yanzu ba a ji ko ganin fuskar shugaban hukumar sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan Agundi ba.
Baffa Babba Dan Agundi wanda tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar dokokin jihar Kano ya kasance na gaba – gaba a jam’iyyar APC Gandujiyya da ke taka rawa a dukkanin wani abu da gwamnati ta ke da muradi akai.
Al’ummar jihar Kano dai sun ga irin rawar da shugaban hukumar ta KAROTA ya taka a lokacin da ake takun saka tsakanin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
To amma a wannan karon tun da aka sa zare tsakanin jiga-jigan jam’iyyar da su ka haɗa da tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibrin da wasu ƴan majalisar wakilai ba a ji ɗuriyar Baffa Babba ɗin ba.

Sai dai wata majiya da ta buƙaci a sakaye sunanta ta bayyanawa Labarai24 cewa a halin da ake ciki akwai rashin jituwa tsakanin Baffa Babba Danagundin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje sakamakon wani fili da ke kan titin zuwa jami’ar Bayero da ke birnin Kano.
“Gaskiya a halin da ake ciki akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Baffa Babba Dan Agundi. Kuma tabbas tsamin dangantakar na da nasaba da wani fili da ake zargin gwamnatin Kano ta karɓe shi daga hannun Baffa Babba ɗin”
Idan za a iya tunawa dai a ranar Talata da ta gabata ne wasu ƙusoshin jam’iyyar ta APC ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha’aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam’iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.