Gwamna El-rufai na shirin sake baiwa Hadiza Bala Usman muƙami

530

Wasu rahotanni daga jihar Kaduna na nuni da cewa akwai yiwuwar Gwamnan jihar Nasiru El-Rufai na jihar ya nada tsohuwar shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta ƙasar nan, wato NPA, Hadiza Bala Usman shugabar ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Hadiza Bala Usman wacce ta taɓa rike muƙamin a wa’adin zangon mulkin farko na El-Rufai daga 2015 zuwa watan Yulin 2016. Kafin daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ta mukamin shugabancin Hukumar Tasoshin Ruwa ta Nijeriya (NPA) a 2016.

Gwamna Nasiru El-rufai da Hadiza Bala Usman

Jaridar Katsina Post ta rawaito cewa gwamna Nasiru El-Rufai zai ba ta mukamin ne biyo bayan matakin sauyawa Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo mukami daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin zuwa Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi mukamin da shima ya taɓa rikewa a baya.

Hadiza Bala dai ita ce wadda ta kirkiro tare da taka rawa a ƙungiyar nan mai fafutukar ganin an ceto ƴan matan Chibok, wato Bring Back Our Girls, tun lokacin tsohon shugaba Goodluck Jonathan

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan